<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Goss, John (1800-1880), Lyte, Henry F. (1793-1847)</author>
<hymn_number>34</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Maɗaukaki na Allah,
 Zan yi yabonka ƙwarai.
 Kai, ka shafe zunubaina,
 Kai, ka ba ni sabon rai,
 Halleluya, Halleluya,
 Girma duka naka ne.

[V2]
 2) Mun yabe ka don alheri
 Zuwa kakaninmu da.
 Yau da gobe ka ke nan fa,
 Ƙaunarka ta tabbata.
 Halleluya, Halleluya,
 Ɗaukaka amincinka,

[V3]
 3) Makiyayi mai tausayi,
 Wanda ya san halinmu,
 Daga dukan jarabobi
 Ya fisshe mu lafiya.
 Halleluya, Halleluya,
 Wa ke jinƙai kamarka?

[V4]
 4) Ɗaukaka ga Ubangiji,
 Kai kaɗai mai adalci,
 Kai ne farko, kai ne ƙarshe,
 Ƙauna, Iko, Gaskiya.
 Halleluya, Halleluya,
 Mun yi maka sujada.</lyrics>
<title>Ya Maɗaukaki na Allah LW34</title>
</song>